Tuesday, 7 May 2019

Kalli abinda Messi yayi bayan da Liverpool tawa Barca aradun kwallaye 4 da ya dauki hankula

Bayan da Liverpool tawa Barcelona aradun kwallaye har 4-0 a wasan zagaye na biyu na kusa dana karshe na cin kofin zakarun turai bayan da a zagayen farko Barca ta wa Liverpool 3-0, An ga tauraron Barca, Messi na yin wani irin kallo da ya dauki hankulan mutane bayan da aka tashi wasan.A yayin da alkalin wasa ya hura usur din karshe, 'yan wasan Liverpool suka runtuma da gudu suna murnar nasarar da suka samu, kyamarorin nan masu gani har hanji na filin wasa sun rika dauko hoton Messi inda aka ga ya ya yamutsa fuska.

Wannan lamari ya dauki hankula sosai.

No comments:

Post a Comment