Sunday, 12 May 2019

Kalli abinda Muhammad Gudaji Kazaure yayi bayan da yaga motocin alfarma na gidan sanata Dino Melaye da ya dauki hankula

Dan majalisa me wakiltar Kazaure/ Roni/Gwiwa, daga jihar Jigawa, Honorabul Muhammad Kazaure Gudaji ya jewa Sanata Dino Melaye gaisuwar mahaifiyarshi da ta rasu, yawan motocin da ya gani a gidan Sanata Melaye sun bashi mamaki sosai inda bidiyon da aka dauka na yanda yake nuna al'ajabinshi ya watsu sosai a shafukan sada zumunta.A wani yanki na bidiyon anji Muhammad Kazaure na cewa, Kai idan ni ke da irin wannan ai zarewa zanyi, nifa idan inada miliyan dari musamman a watan azuminnan to miliyan 80 abinci zan saiwa mutane dasu.
No comments:

Post a Comment