Monday, 13 May 2019

Kalli abinda Pogba yawa wasu fusatattun magoya bayan Man U da suka zageshi


Paul Pogba
Bayan rashin nasarar da Manchester United ta yi jiya, lahadi a hannun Cardiff City da ci 2-0, wasu fusatattun magoya bayan Man U sun zagi tauraraon dan wasan kungiyar, Paul Pogba inda shi kuwa Pogban ya mayar masu da martani.

Pogba ya daga kafadarshi sannan yayi murmushi ya kuma dagawa wanda suka zageshin babban dan yatsa.

Saidai tsohon dan wasan kungiyar, Alan Shearer ya bayyana cewa da Pogban da be biyewa fusataccen magoyin bayan ba, dama beje kusa da su ba ya wuce abinshi.

No comments:

Post a Comment