Thursday, 16 May 2019

Kalli mutumin da ya fara sayen mota a Kano

Wannan shine, Ali Bin Alua dake zaune a gefen me zaman banza a cikin motarshi kirar Fodi. Shine mutum na farko da ya fara mallakar mota a jihar Kano.Dan kasuwane daya fito daga kasar Libya kuma ya zauna a Kano a wajan shekarun 1878, hakanan shine mutum na farko daya fara gina gidan bene a Kano. A wajan farkon karni na 20 shine mutumin da yafi kowa kudi a yankin Arewa. Ya mutu a shekarar 1958.


No comments:

Post a Comment