Sunday, 5 May 2019

Kalli yanda aka kama wani da sandunan guragu ya boye kwaya a kafarshi cikin bandeji

Wani hoton bidiyon da ya nuna yanda aka kama wani mutum a wata kasar Larabawa da sandunan guragu da bandeji a kafarshi, ashe cikin bandejin kwayace, ya yadu sosai a shafukan sada zumunta.Da dama sun bayyana cewa a kasar Saudiyya aka kama mutumin amma babu wata alama data tabbatar da hakan.

An ga dai hoton bidiyon dake nuna yanda wasu larabawa ke warware kafar mutumin suna zaro kwayoyin da ya boye a ciki.

No comments:

Post a Comment