Wednesday, 8 May 2019

Kalli yanda kocin Tottenham ya fashe da kukan murna: Karanta abinda ya gayawa 'yan wasanshi akan Liverpool

Bayan da Tottenham ta lallasa Ajax da ci 3-2 a wasan da suka buga a daren yau na zagaye na biyu na kusa dana karshe na cin kofin Champions League, Me horas da kungiyar ta Tottenham, Mauricio Pochettino ya kasa rike murnarshi inda dan tsananin murna har kuka sai da yayi.
Kamin fara wasan, dan kasar Argentinan ya gayawa Being Sport cewa gaskiya ba karamar mu'ujizace zata sa su ci kofin na Champions League ba, saidai bayan wasan cikin farin ciki yace ya godewa kwallo dan itace kawai zata iya sakashi cikin irin wannan yanayi na shauki.

Danny Rose ya bayyana cewa kamin wasan, Mauricio Pochettino ya gaya musu cewa kunga dai yanda Liverpool ta dage ko? Bawai zaku dauka an fitar daku bane dagewa zaku yi har sai an tashi munga yanda hali yayi.

Yace kocin ya basu karfin gwiwa sosai inda ya basu misali da bajintar da Liverpool suka nuna a wasansu da Barcelona jiya.
No comments:

Post a Comment