Friday, 17 May 2019

Karanta Abinda gwamnan Borno yace akan raba masarautar Kano

Gwamnan jihar Borno Khashim Shattima ya bayyana ra'ayinshi akan raba masarautar Kano da gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi inda yace shi baiga aibun hakan ba.
Shattima ya bayyana hakane a yayin da kwamiti akan soji na majalisar wakilai suka kai mishi ziyara kamar yanda Channels ta ruwaito. Inda yace shi baiga wani abin tayar da hankali akan raba masarautar ta Kano ba.

Yace akwai matsalolin Najeriya da ya kamata ace ana magana akansu ba wai maganar raba masarautar Kano ba.Ya kara da cewa matsalar mutanen mu kenan, babu wani abu na musamman a tattare da Sarkin, Injishi.

A koda yaushe sai a rika watsa labaran da basu kamata ba akan Arewacin Najeriya alhalin akwai matsalolin da muke fama dasu. An yi kiyasin cewa nan da shekarar 2050, kashi 70 na mutanen Najeriya zasu kasancene a Arewacin Kasar. Da irin matsalolin da muke ciki ba za'a taba samun zaman lafiya ba idan babu ci gaba. Ilimi shine babban makamin magance wadannan matsaloli, inji Gwamnan.

No comments:

Post a Comment