Saturday, 11 May 2019

Karanta martanin dan Sarkin Kano akan kirkirar karin masarautun da Gwamnatin jihar ta yi

Dan me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II, Ashraf Sanusi ya mayar da martani akan kirkirar sabbin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta yi, inda yace yana ta samun sakwanni akan lamarin amma abinda zai gayawa masoyan mahaifinshi shine kada wanda ya zagi wani wajan bayyana ra'ayinshi akan wannan lamari.Ashraf ya bayyana hakane ta shafinshi na Instagram inda ya fitar da sakon:
 Yace na samu sakwanni da dama kan lamarin dake faruwa wanda na tabbata duk kunsan dashi. Na yi imanin cewa abu irin wannan kamata yayi abarshi a hannun mutanen da ke da ilimi da kuma sanin yanda ake warwareshi. Ni ba kwararre bane a harkar siyasa ko kuma bayar da shawara, ina godiya ga wadanda suke goyon bayan mahaifina amma kirana a gareku shine kada wanda ya zagi wani wajan bayyana ra'ayinshi, kada kuma wanda ya dauki yanke wata tsatstsaurar shawara akan wannan lamari ba tare da yasan ainahin me ake ciki ba.

Kada ku tsani kowa saboda ya nunawa wani fifiko dan watakila shima be san ainahin yanda lamarin yake ba. Mu yi abinda ya kamata, mu jajirce akan lamurran rayuwarmu sannan sai mu barwa Allah sauran.

Muna fatan duk wanda yake akan gaskiya tsakanin Sarki da Gwamna ya samu nasara, mahaifina ya fadi abinda ke cikin zuciyarshine a lokacin da ya ga ya kamata yayi hakan, a ganina hakan ba kuskure bane. Idan aka saukeshi daga mukaminshi ko kuma aka rage mai karfi, fatan da zan wa mutanena shine Allah ya baku shugaba me adalci kamarshi.

Idan kuma ya samu karin daukaka ina fatan zai ci gaba da kasancewa adali. Allah ya zabawa mutanen mu abinda yafi Alheri.Amin

No comments:

Post a Comment