Wednesday, 8 May 2019

Karanta yanda Motar data dauki 'yan wasan Barcelona ta bar Messi a filin wasan Liverpool

Bayan kammala wasan zagaye na biyu na kusa dana karshe na gasar cin kofin zakarun turai da aka yi tsakanin Liverpool da Barcelona jiya, motar da ta dauki 'yan wasan Barcelona ta bar tauraron kungiyar, Lionel Messi a filin wasan Liverpool.El Chiringuito ta ruwaito cewa, bayan wasan an bukaci yiwa Messin gwajin tantance ko ya sha kwayoyin kara kuzari, gwajin ya dauki lokaci ta yanda yasa bai samu bin motar da ta dauki 'yan wasan na Barcelona zuwa filin jirgi ba suka barshi a filin wasan na Anfield.

Messi ya bayar da samfurin fitsarinshi dan yin gwajin, sai daga baya aka kaishi suka hadu suka tafi tare.


No comments:

Post a Comment