Friday, 10 May 2019

Karanta yanda ta kaya tsakanin Messi da wasu fusatattun magoya bayan Barcelona bayan cin da Liverpool ta musu

Bayan da tauraron dan kwallon Barcelona, Lionel Messi ya bar filin wasan Liverpool bayan lallasasu da Liverpool din ta yi da ci 4-0, ya isa filin jirgin sama, ya gamu da wasu magoya bayan Barcelona da suka yi cece-kuce dashi.Magoya bayan Barcelonar sun rika cemai, Messi kai ne fa Kyaftin, kai ya kamata ka ja ragamar kungiyar, kamar yanda gidan talabijin na El Chiringuito ya ruwaito.

Sun ci gaba da cewa, haba! Gaba daya shekarar nan Marc-Andre Ter Stegen aka rika amfani dashi a matsayin gola.

Saidai Messin ya rika basu amsar cewa, me na yi? Wai me nayi? Akai akai.

No comments:

Post a Comment