Monday, 6 May 2019

Karanta yanda ya yiwa mahaifiyarshi karya ta kare akanshi

Wata baiwar Allah ta bayar da labarin yanda mahaifiyarsu ta ari shahararren abin kunnennan na kamfanin Apple da ake kira da Airpods a turance daga hannun dan uwanta. Tace bayan mahaifiyar tasu ta yi amfani dasu kuma ta ji dadinsu sai ta tamba yi dan nata nawa ake sayar dasu?


Saboda tsoron kada ta mai fada sai ya ce mata dubu 12 suke. Nan ta bashi dubu 12 ta ce ya je ya sayi wasu ita zata rike wadannan.

Wannan lamari ya dauki hankulan mutane.

Farashin Sabon Airpods na asali a Najeriya yakan kai a kalla dubu 60.  

No comments:

Post a Comment