Saturday, 4 May 2019

Kasa da awa 24 bayan da yayi magana akan 'yan bindiga: 'Yan bindigar sun kai hari gidan Bafarawa, sun kashe mutum daya da kuma sace dan uwanshi


A former governor of Sokoto State, Alhaji Attahiru Bafarawa
'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa inda suka kashe me gadinshi, Abdullahi Jijji sannan suka yi garkuwa da wani dan uwanshi me shekaru 16, Abdulrasheed Sa'idu.

Lamarin ya farune a daren jiya, Juma'a wajan karfe 9 na dare, sannan wannan hari na zuwane kasa da awanni 24 bayan da tsohon gwamnan ya kaddamar da wata gidauniya a Abuja da ya sakawa sunanshi inda yace zata taimaka wajan magance matsalar 'yan bindiga da satar mutane da ake yi musamman a Arewacin kasarnan.

Daraktan gidauniyar Bafarawa, Dr. Sulaiman Shu'aibu ya tabbatar da wannan lamari ga jaridar Daily Trust inda yace 'yan bindigar sun zo ne su kusan 60 akan babura dauke da bindigogin Ak47, da jaridar ta tuntubi me magana da yawun 'yansandan jihar Sakkawato DSP Muhammad Sadik yace be san da faruwar wannan lamariba.

No comments:

Post a Comment