Monday, 13 May 2019

Kirkirar sabbin masarautun da Ganduje yayi abune me kyau>>Dr. Junaidu


Tsohon dan majalisar tarayya, Dr. Junaidu Muhammad ya yabawa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa kirkirar karin masarautu a jihar ta Kano inda yace idan gwamnan be yi ba to wanene zai yi hakan?

Dr. Junaidu ya bayyana hakane a hirar da yayi da jaridar Vanguard inda yace shi baiga laifin Gwamnan ba dan ya saurari bukatar mafi yawan mutanen jihar kuma ya cika musu burin su, ya kara da cewa gwamnan be karya doka ba wajan kirkirar wadanan sabbin masarautu kuma abune da mafi yawan mutanen Kano suka jima suna nema.

No comments:

Post a Comment