Sunday, 12 May 2019

Ko kadan hankaline be tashi da wasan yau ba: Guardiola ya hana 'yan Man City duba sakamakon wasan Liverpool

Me horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya bayyana cewa ko kadan hankalinshi be tashi ba dangane da wasansu na yau da zasu buga da Brighton wanda idan suka yi nasara sun dauki kofin Premier League sau biyu a jere kenan.Idan kuwa suka yi rashin nasara, to Liverpool na iya daukar kofin idan ta yi nasarar cin Wolves.

Guardiola yace baccinshi yayi kamar karamin yaro, kuma be cewa 'yan wasanshi komai ba, babu wata maganar karfafa gwiwa da zai musu, dan ya gani a tattare da su akwai karsashin son daukar kofin na Premier lokacin da suke atisaye.

Yace basu maganar sake daukar kofin na Premier, ko kuma yanda zasu yi murna idan suka dauki kofin, yace abinda ke gabansu shine inane mamorar Brighton sannan ta wane bangarene suke da karfi, yaya suke tare dadai sauransu.

The Sun ta ruwaito cewa, Guardiola ya hana ma'aikatan Manchester City kallo da kuma duba sakamakon wasan Liverpool, rahoton yace Me horas da 'yan wasan na bukatar duk su maida hankaline wajan yin nasarar wasansu kawai.

No comments:

Post a Comment