Wednesday, 15 May 2019

Kotu ta dakatar da EFCC daga binciken Saraki

Babbar kotun gwamnatin tarayya dake babban burnin tarayya, Abuja ta dakatar da hukumar hana yiwa arzikin kasa zagon kasa, EFCC daga binciken da takewa kakakin majalisar dattijai,Sanata Bukola Saraki.Saraki dai ya shigar da kara inda yake kalubalantar binciken da hukumar ke mai.

Alkalin kotun ya ce EFCC ta dakata da binciken da takewa Saraki har sai an gama sauraren shari'ar tukuna.

An ruwaito cewa, EFCC ta fara binciken Saraki inda tuni har ta kwace wasu gidaje mallakinshi.

No comments:

Post a Comment