Wednesday, 15 May 2019

Kotu ta dakatar da nadin sabbin sarakunan Kano

Babbar kotun jihar Kano ta dakatar da sarakunan da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro. Inda tace ta dakatar da sabbin sarakunanne har sai an kammala shari'ar dake gabanta da aka shigar da wasu ke kalubalantar nadin sarakunan.A ranar talatane dai wasu da aka bayyana a matsayin masu nadin sarki a Kano suka shigar da kara inda suke kalubalantar nadin da gwamnan yawa sarakunan da cewa ya lalata al'adar kaka da kakanni da aka santa a Jihar sannan ba ma shi da hurumin yin wancan nadi.


No comments:

Post a Comment