Tuesday, 14 May 2019

Ku daina yin barkwanci dani>>Shugaba Buhari ya gargadi 'yan Najeriya


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya aikewa da 'yan najeriya musamman masu harkar nishadi da shirya fina-finai da su kiyayi yin barkwanci dashi.

Ya kara da cewa kowace kasa nada matsalolin dake damunta amma 'yan kasar basa maganganun shashanci akan shuwagabanninsu.

Shugaban ya kuma yi magana akan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar dake kalubalantar nasarar zaben da ya samu a kotu, inda ya tabbatar da cewa idan Atikun yayi nasara a kotun zai sauka daga mulki ya bashi, Kamar yanda Independent ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment