Saturday, 11 May 2019

Kwallon 'yan Matan Africa: Najeriya ta ci Nijar 15-0

Kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya, Super Falcons sun lallasa kasar Jamhuriyar Nijar da kwallaye 15-0 a wasan da suka buga yau Asabar na gasar kwallon 'yan matan Afrika.Wannan yasa suka kafa tarihin cin kwallaye mafi yawa a gasar kwallon 'yan mata ta nahiyar Africa. Gasar kwallon 'yan matan da ake yi a birnin Abidjan na kasar Kwadebuwa na samun halartar kasashe 8 na yankin Yammacin Afrika.

No comments:

Post a Comment