Thursday, 30 May 2019

Kwana daya da rantsar dashi Gwamnan Yobe ya kara aure na 3

Sabon gwamnan jihar Yobe da aka rantsar jiya,Mai Mala Buni ya angwance kwana daya da rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar ta Yobe inda ya auri diyar gwamnan da ya sauka ya bashi kujera.Rahoton Daily Nigerian na cewa, Maimala Buni ya auri diyar tsohon gwamna Ibrahim Gaidam me suna Ummi Adama Gaidam a yau Alhamis inda aka daura auren cikin sirri a gidan tsohon gwamnan dake unguwar sabon Fegi, Damaturu.

Ummi da yanzu haka ke karatu a kasar Saudiyya ta zama matar gwamna Maimala Buni ta 3 kenan.

Gwamna Gaidam dai ya nuna goyon bayanshi ga Mailama Buni a takarar gwamnan jihar da yayi. Kuma rahotannin sunce Maimala Buni ne ya nemi auren Ummi ba ma tare da mahaifinta ya sani ba.

No comments:

Post a Comment