Wednesday, 1 May 2019

Liverpool ce kadai Messi bai ci ba a Ingila


Messi
Liverpool ce ka dai kungiyar Ingila da Lionel Messi bai ci ba a gasar Zakarun Turai, za kuma su hadu ranar Laraba a gasar Champions League.


Liverpool za ta ziyarci Barcelona a Nou Camp a wasan farko na daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai ta bana.
Kawo yanzu Messi ya ci kungiyoyin Ingila kwallo 24 da ya zura a ragar Manchester City da United da Arsenal da Chelsea da kuma Tottenham jumulla.
Barcelona ta lashe kofin La Liga na bana, kuma Messi ke gan gaba a yawan cin kwallo a Spaniya, bayan da ya zura 34 a raga ya kuma ci kofin La Liga na 10 a Nou Camp.
Ga jerin kwallayen da Messi ya ci kungiyoyin Ingila:
Chelsea
Karawa 10 ya yi da kungiyar
Ya ci kwallo 3
Messi
Messi ya ci Chelsea kwallo a bara, bayan da Andreas Christensen ya yi kuskure, inda dan Argentina ya ci kwallo a karawar da suka tashi 1-1 a wasan zagayen farko na kungiyoyi 16.
A wasa na biyu ne da suka kara a zagaye na biyu, Messi ya ci kwallo biyu a karawar da Barcelona ta yi nasara da ci 3-0.
Arsenal
Karawa 6 ya yi da Gunners
Ya ci kwallo 9
Messi
Messi ya ci Arsenal kwallo hudu a wasan farko na daf da na kusa da na karshe a watan Afirilun 2010, a lokacin da Arsene Wenger ke jan ragamar Gunners.
Jumulla kwallo tara ya zura a ragar Gunners, kuma ita ce kungiyar da dan wasa ya zura kwallaye masu yawa a gasar Zakarun Turai.
Manchster City
Karawa da kungiyar 6
Kwallayen da ya zura a raga 6
Messi
Cikin kwallayen da Messi ya ci Manchester City har da uku rigis da ya zura a raga a wasan rukuni na uku a Camp Nou karkashin jagorancin Pep Guardiola.
Manchester United
Karawar da kungiyar 6
Kwallaye da ya ci kungiyar 4
Messi
Kwallo hudu Messi ya ci Manchester United da suka hada da a wasan karshe da ya ci da ka a 2009 da kuma wata ta kasaita da ya zura a raga a kakar 2011.
Sai kuma biyun da ya ci United a wasan daf da na kusa da na karshe a watan Afirilu.
Tottenham
Karawar da ya yi da kungiyar 2
Kwallayen da ya ci 2
Messi
Wannan kakar ce Tottenham da Barcelona suka fara karawa, inda aka hada su rukuni na biyu a gasar Champions League.
Messi ya ci kwallo biyu ne a wasan da suka tashi 4-2 da Tottenham a Wembley.
Liverpool
Karawar da ya yi da kungiyar 2
Bai ci kwallo ba.
Messi
Messi ya fuskanci Liverpool a wasan zagaye na biyu a gasar Champions League karawar zagaye na biyu, a lokacin dan kwallon tawagar Argentina yana da shekara 19 a kakar 2006-7.
Messi ya buga dukkan fafatawar biyu kuma da shi aka karkare wasannin da Liverpool ta yi nasara da ci 2-1 a Nou Camp, amma ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0.
Messi na fatan lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na bana wato Ballon d'Or, bayan da Barcelona ta ci La Liga ta kai daf da karshe a Champions League za ta buga wasan karshe a Copa del Rey.
Shin ko Messi zaui ci Liverpool kuwa a wannan karon?
BBChausa.

No comments:

Post a Comment