Saturday, 18 May 2019

Mace marar hannaye ta farko data samu lasisin tuka jirgin sama a Duniya: Kalli yanda take tuka jirgin da kafarta

Jessica Cox kenan 'yar shekaru 36 wadda aka haifa babu hannu amma kuma ta samu nasarori a rayuwa wanda da dama daga cikin masu hannaye biyu basu samu ba. Babban abinda ya dauki hankulan mutane akan Jessica Cox shine yanda take tuka jirgin sama da kafarta.'Yar asalin jihar Arizona dake kasar Amurka ta samu shiga kundin ababen bajintar Duniya saboda nasarorin da ta samu a rayuwarta,sannan ta shiga manya-manyan kafafen sadarwa na Duniya irin su, CNN, CBS, Fox dadai sauransu.

Itace mace ta farko marar hannaye da ta samu lasisin tuka jirgin sama a Duniya,. A lokacin da take bayar da labarin yanda aka haifeta, tace mahaifiyarta ta yi laulayin ciki irin wanda aka saba gani. Saidai duk mahaifan nata biyu sun shiga yanayin damuwa bayan da likita ya kawo musu ita babu hannaye. Saidai wannan be hanata cimma burikan rayuwarta ba.

Tana da digiri akan sanin halayyar dan Adam, ta iya tuka mota da jirgin sama, ta iya buga Piano ta kuma samu kambun bajinta na damben Taikwando. Wata kungiya me zaman kantace ta dauki nauyin karatunta na zama me tukin jirgin sama.

Ta ziyarci kasashen Duniya 23 inda ta gabatar da jawabi akan karfafa gwiwar cimma burikan rayuwa inda take bayar da misali da rayuwarta.

No comments:

Post a Comment