Monday, 20 May 2019

Mafusata Sun Kone Masu Garkuwa Da Mutane Kurmus A Jihar Kaduna

Wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun gamu da gamuwar su a kusa da gidan man Nipco tsohuwar gidan man Lalan dake Kawo Kaduna.


Mutanen Dai Ana Zargin Cewa Masu Garkuwa da Mutane ne Inda ake zargin sun sato wani bawan Allah ne a Sabon Kawo dake Kawo Kaduna. Inda masu babura suka biyo su da ihu har zuwa bakin gidan man Lalan.

Nan fa matasa suka ce da waye Allah ya hada su in ba da su ba.

Kafin jami'an 'Yan sanda su iso wajen har an kashe daya daga cikinsu inda aka kona shi tare da motar su kirar Sharon.

Daga baya an ji wani alamun kamar na bindiga yana tashi a cikin motar.

Mun yi kokarin ganin wanda aka sato din amma abun ya ci tura domin ba mu san inda ya shige ba.

Su ma jami'an 'Yan sanda da suka iso wajen abun ya riga ya sha karfin su, domin aikin gama ya riga ya gama.

Koma dai da mene ne, sai mu ce Allah ya tsare mu baki daya.
Rariya.


No comments:

Post a Comment