Wednesday, 22 May 2019

Magajin garin Daura ya cike sati 3 a hannun masu garkuwa dashi

Magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba ya cika sati 3 kenan a hannun masu garkuwa da mutane da suka je har gida suka saceshi.Ranar Laraba, 1 ga watan Mayu ne da yamma bayan sallar Magariba, masu garkuwa da mutanen suka shiga garin Daura inda suka yi harbi a iska sannan suka sace magajin garin a cikin mota kirar Peugeot 406.

Wasu mutanen garin Daura da Premiumtimes ta yi hira dasu sun bayyana cewa har yanzu basu dawo daidaiba kuma Magajin Gari mutum ne na jama'a dan haka wadanda suke tare da shi suna kewar rashinshi.

Wani kuwa cewa yayi sun yi mamakin ganin cewa babban mutum kamar magajin gari zai yi irin wannan dadewar a hannun masu garkuwa da mutane ba tare da an amsoshi  ba.

Da aka tuntubi hukumar 'yansanda ta bayyana cewa tana kan bincike kuma har ta kama mutane.

No comments:

Post a Comment