Wednesday, 15 May 2019

Mai yiwuwa Bale zai koma tsohuwar kungiyarsa a matsayin aro

Real Madrid ta gabatarwa da kungiyar Tottenham tayin mika mata tsohon wasanta Gareth Bale a matsayin aro kan euro miliyan 10.A shekarar 2013, Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham kan euro miliyan 86, abinda ya sa shi zama dan wasa mafi tsada a waccan lokacin.

Tun daga waccan lokacin Bale ke kan gaba wajen samun albashi mai tsoka tsakanin takwarorinsa a kungiyar ta Real Madrid, inda a yanzu haka yake amsar fam dubu 600 a mako daya.

Sai dai a baya bayan nan, dan wasan na fuskantar kalubalen nuna kwazo a wasannin da yake bugawa, lamarin da yasa yake fuskantar suka daga mafi akasarin magoya bayan Real Madrid, hakan tasa dillalinsa a watannin baya, ya zargi magoya bayan da nuna butulci kan gudunmawar da Bale ya basu wajen lashe kofunan gasar Zakarun Turai a shekarun 2014 da kuma 2018.

Yarjejeniya tsakanin Bale da Real Madrid za ta kare a shekarar 2022, amma a halin yanzu, kungiyar ta ce a shirye take ta mika shi ga kowace kungiya a matsayin aro, muddin za ta biya euro miliyan 10 kuma ta rika biyan dan wasan albashin fam dubu 250 a mako daya.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment