Saturday, 18 May 2019

Maimakon Griezmann, Messi ya bukaci Barcelona ta siyo tauraron Premier League


Bayan da tauraron dan wasan Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya bayyana cewa zai bar kungiyar, akwai magana me karfi dake dangantashi da komawa Barcelona. Saidai ga dukkan alamu hakan ba zata yiyu ba saboda Messi be so a sayoshi.

Fox Sports ta ruwaito cewa har yanzu Messi na kule da Antoine Griezmann akan kin komawa Barca da yayi tun a kakar wasan data gabata da suka neshi dan haka yace a barshi kawai a siyo tauraron Premier League.

Wanda Messi ke so a siyo a Premier League shine tauraron kungiyar Tottenham watau Harry Kane.

No comments:

Post a Comment