Wednesday, 22 May 2019

Manchester United na neman sayen Ivan Rakitic daga Barcelona

Kungiyar Manchester United na kokarin ganin ta sayo tauraron Barcelona, Ivan Rakitic dan ganin ta maye gurbin Ander Herrera, dadin dadawa gashi babu tabbacin Paul Pogba zai tsaya a kungiyar.Daily Record ta ruwaito cewa Manchester United na neman sayen dan wasan tsakiyar na Barca ruwa a jallo dan ganin sun maye gurbin Ander Herrera.

Duk da yake cewa Rakitic ya shafe shekaru 5 yanawa Barca wasa amma suna son sayar dashi dan su samu kudin sayen wasu 'yan wasan, ko da ma dai ya zauna a kungiyar ba lallaine ya samu rika buga wasa kamar da ba saboda zuwan Frenkie de Jong.

Barcelona na bukatar fan milyan 48 akan Rakitic saidai Man U na kokarin ganin ta sayeshi akan fan miliyan 30. Koda korarren kocin Man U, Jose Mourinho ya so ya sayi Rakitic a baya inda ya bayyanashi a matsayin dan wasan da ba ya samun yabon da ya kamata.

No comments:

Post a Comment