Wednesday, 15 May 2019

Masu ruwa da tsaki a nadin sarautar Kano sun maka gwamna Ganduje a kotu

Masu ruwa da tsaki akan nadin sarauta a Kano daga fadar sarkin Kanon, sun maka  gwamnan Kanon, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a kotu inda suke kalubalantar sabbin masarautun daya kirkiro kwanannan.Karar da aka shigar jiya Talata a babbar kotun jihar ta Kano na tuhumar gwamnan Kanon da me baiwa gwamnan shawara akan harkar shari'a da kuma sauran wasu mutum biyar.

Wadanda suka shigar da karar sune, Yusuf Nabahani (Madakin Kano), Abdullahi Sarki Ibrahim (Makaman Kano), Bello Abubakar (Sarkin Dawaki man Tuta) and Mukhtari Adnan (Sarikin Ban Kano) 

Suna tuhumar gwamnan da laifin lalata dadaddiyar al'adar jihar da aka sani kaka da kakanni ta hanyar kirkirar sabbin masarautun da yayi.

Karar tace gwamnan bashi da hurumin kirkirar masarautun da yayi.

No comments:

Post a Comment