Wednesday, 8 May 2019

Matashi ya kashe kanshi wajan murnar nasarar da Liverpool ta samu akan Barca

Wani matashi dake goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya kashe kanshi har lahira wajan murnar nasarar da Liverpool din ta samu jiya akan Barcelona a wasan da suka buga na kusa dana karshe na cin kofin Champions League.Matashin dan kasar Ghana me suna Hebert Danso Atiko yana rubuta jarabawarshi ta karshene a makaranta. Bayan kammala wasan yana cikin murna kawai sai aka ga ya fadi kasa cikin wani irin yanayi.

An garzaya dashi asibiti amma sai likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.

No comments:

Post a Comment