Monday, 13 May 2019

Me horas da Barcelona ya bayyana yanda Messi ke kokarin murmurewa daga rashin nasarar da suka yi a hannun Liverpool


Liverpool defeat left a bad taste in Messi's mouth, admits Valverde
Me horas da kungiyar Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana cewa, sakamakon wasan da suka buga da Getafe ya nuna cewa sun fara murmurewa daga kaduwar da fitar dasu da Liverpool ta yi daga gasar Champions League.

Barcelona ta sakawa Getafe kwallaye 2-0 a raga wanda kuma haka aka tashi wasan.

Yace da wannan nasarar kowa zai kara samun karsashi duk da yake cewa da farko munsha wuya. Yace akwai wasan Copa Del Rey a gabansu.

Ya kara da cewa, Messi na kokarin ganin ya murmure daga rashin nasarar da suka yi a hannun liverpool. Dukan mu mun yi tsammanin zamu kai wasan karshe na Champions League amma hakanan zamu hakura.

No comments:

Post a Comment