Friday, 24 May 2019

Messi yayi magana akan barin Barcelona saboda rashin nasararsu a hannun Liverpool a gasar Champions League: Yace lamarin ya tabashi sosai


Sati 3 bayan ragargazar da Liverpool tawa Barcelona na ci 4-0 a zagaye na biyu na wasan kusa dana karshe na gasar Champions League wanda gaba daya 4-3 kenan idan aka hada da wasan zagayen farko, tauraron Barcelona, Lionel Messi ya bayyana yanda ya ji radadin abin a zuciyarshi.


Nasarar da Liverpool ta samu itace irin ta ta farko a tarihin kwallon kafa da aka taba samun wata kungiya da aka ci kwallaye 3 a zagayen farko na wasan kusa dana karshe na wata gasa sannan a zagaye na biyu ta farke kwallayen ta kuma kai ga wasan karshe.

Wannan wasan na zuwane shekara daya bayan kwatankwacin haka ya faru da Barcelona a wasan da suka buga da Roma inda a zagayen farko Barcelonan ta ci kwallaye 4-1 amma a zagaye na biyu Roma ta ci 3-0. Messi da Barcelona sun sha suka sosai a kafafen watsa labaran Sifaniya akan wannan lamari.

An ruwaito cewa Messi sai da ya zubar da hawaye a dakin canja kaya na 'yan wasa a filin wasan Liverpool bayan kammala wasan, bayan da mafarkin da yake dashi na kamo babban abokin takararshi, Cristiano Ronaldo a yawan kofin Champions League ya zo karshe.


Messi yace gaskiya abin ya taba su sosai, ya ci gaba da cewa dole mu bayar da hakuri akan yanda zagaye na biyu na wasan ya kasance, yace ko da badan yanda sakamakon wasan ya kasance ba, amma kwata-kwata basu yi kokariba.

Ya kara da cewa lamarin yana daya daga cikin abubuwa mafi muni a tarihin buga kwallonshi.

Saidai Messi yace lashe kofin Copa del Reys zai zamar musu hanya mafi kyau ta kammala kakar wasan 2018/19.

Messi ya kuma kare me horas da 'yan wasan Barcelona, Ernesto Valverde inda yace rashin nasarar da suka samu ba laifinshi bane, laifin 'yan wasanne kuma zai so Ernesto Valverde din yaci gaba da zama a Brcelona.

Da aka tambayeshi ko yana tunin barin Barcelona?

Sai yace a'a ko kadan, na samu matsala da kungiyar kwallon kafar kasata amma duk da haka na ci gaba da kokarin ganin yin nasara acan, dan haka cire mu daga gasar Champions League ba zai sa in bar Barcelona ba.


No comments:

Post a Comment