Saturday, 18 May 2019

Motocin tirela masu tuka kansu dake aiki da lantarki sun fara yawo a kasar Swidin

Motocin tirela marasa matuki dake aiki da lantarki sun fara yawo a garin Jonkoping na kasar Swidin.


Daya daga cikin motocin ta yi kewaye a yankin Masana'antu dake Jonkoping kuma ta dauki kaya a cikinta wadda aka dinga sarrafa ta daga nesa.

Darakta Janar na kamfanin Einride da ya kera motar Robert Falck ya fadi cewar a karon farko a duniya motar tirela mara matuki ta fara aiki da lantarki, kuma sun ba ta sunan T-Pod.

Falck ya kara da cewar motar na aiki da fasahar sadarwa ta G5 kuma tana iya gani a matakin digiri 360 wato ta kowanne bangare.

Darakta Falck ya kara da cewar motar tirelan na da saukin kashe kudi da kula da ita, şnda ya ce ta fi mai aiki da direba da mai sauki da kaso 60 cikin dari.

Ya kuma ce, an dauki dukkanin matakan yadda 'yan ta'adda ba za su yi amfani da motar ba wajen kai hari.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment