Tuesday, 14 May 2019

Mutune Dubu 524,315 Ne Suka Nemi Aikin Kwastam Cikin Mutune 3,200 Da Za Su Dauka A Duk Fadin Nijeriya

Hukumar hana fasa kwabri ta kasa da ake kira da kwastam ta yi karin haske game da jami'an da za ta dauka na cike gurbin mutum 3,200 a duk fadin Nijeriya a wannan shekarar ta 2019.


Jami'in hulda da jama'a na hukumar Mr Joseph Attah ya ce kawo yanzun wadanda suka cike aikin bisa ka'ida sun kai 524,315, kuma za a dauki aikin ne bisa cancanta ba tare da nuna son kai ba.

Za a iya tuna cewa a ranar 17 ga watan April 2019 ne hukumar ta bude fara daukar ma'aikatan cike gurbi guda 3,200 a hukumar ta kwastam.

Daga ciki mutum 800 sune za a dauka Sufiritanda Cadre sai kuma 2,400 Insifeto da sauran cadre din Sai dai a yanzun NAN ta rawaito cewa mutum 278, 582 ne suka cike neman Sufiritanda Cadre sauran kuma kuka cike neman Insifeto da sauran mukaman da za a dauka na kasa.

Daga karshe jami'in hulda da jama'a na hukumar ya ce mutum 828,333, suka yi rijistar neman shiga aikin amma 524,315 kadai rijistar su da yi daidai bisa ka'idar da ake bukata


No comments:

Post a Comment