Thursday, 9 May 2019

” Na san nauyin dake kaina a matsayina na shugaban kasa kuma na san abinda nake yi”>>Inji Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban Najeriya yana sane da irin ayyukan da mutane ke bukata ayi musus kuma ya san abinda yake yi.


Buhari ya fadi haka ne bayan halartar tafsirin Alkur’ani a masallacin fadar shugaban kasa.

Buhari ya ce aikin sa ne ya sa a gaba ” Kuma zamu tabbata mun cika alakwurran da muka dauka wa ‘yan Najeriya.”

Shugaban Buhari dai yana ta shan caccaka daga mutanen Najeriya musamman game da tabarbarewar tsaro a yankin Arewa Maso Yamma.

Idan ba a manta ba Sarkin Katsina ya aika wa shugaba Buhari da sako irin haka inda ya yi kira ga shugaban kasan da ya maida hankali kan matsalar tsaro a jihar Katsina da kasa baki daya domin kawo ayyukan mahara da masu garkuwa.
Premiumtimeshausa.


No comments:

Post a Comment