Tuesday, 21 May 2019

NASIHOHI MASU AMFANI

KADA KA YI RIGIMA DA MUTUM UKU
Mahaifi 
Malami 
Shugaba 


2 MUTUM UKU DA MUTANE BA SA KAUNA
Mai kudi marowaci 
Talaka mai girman kai
Mai neman rigima bashi da karfi. 

3 HALIN MANYA UKU NE 
Yin afwa ga wanda ya zalunce ka
Ka bawa wanda ya hana ka 
Sada zumunta ga wanda ya yanke maka.
KA DARAJA MUTANE UKU A DUNIYA
1. Dattijo.    
2. Malami   
3. Iyaye      
KA TAUSAYAWA MUTUM UKU 
1. Tsoho   
2. mace.    
3. Yaro karami  
KADA KA MANTA ABU UKU 
1. Mutunci   
2. addini.    
3. Mutuwa.    
4. KA TSAFTACE ABU UKU
5. Jikinka     
6. Tufafinka 
7. Zuciyarka.     
KADA KA DENA NEMAN ABU UKU 
1. Ilimi          
2. arziki.    
3. Aljanna. 
ABU UKU SUNA KARA IMANI 
1- Tilawal Al-Qur'ani.
2- Kiyamul-laili.
3- Azkhar.

ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU UKU:

1- Hakkin Wani
2- Dabi'ar Annamimanci
3- Hassada

ABUBUWA UKU SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:

1- Istigfari.
2- Tausayawa waninka
3- Sadaka

IDAN ALLAH YA BAKA ABU UKU TO KA GODEWA ALLAH: 

1- Lafiya
2- Wadata
3- Basira

KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA UKU:

1- Mai yawan fushi.
2- Maras sirri
3- Marar tsafta (Kazamiya)

KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU UKU:

1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana.
3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa

ABUBUWA UKU KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:

1- Yanke Zumunta.
2- Zagin Sahabbai.
3- Mutuwa da hakkin wani

MUTANE UKU KADA KA SAURARI MAGANARSU:

1- Makaryaci
2- Magulmaci
3- Malami mai kwadayi da son zuciya

MUTUM UKU KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA:
1- Munafiki
2- Mazinaci
3- Maras kunya

ABUBUWA UKU BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:

1- Sallah
2- Aure
3- Jana'iza

ABUBUWA UKU RIKO DA SU YANA SAMAR DA RABO A LAHIRA:

1- Kokarin ibada
2- Kula da Nafila
3- Amfani da Halal a Rayuwa

ABUBUWA UKU SUNA HANA MUTUM TANADIN LAHIRA:

1- Dogon Buri.
2- Rashin karanta Alkur'ani
3- Nisantar sauraron Wa'azi.

MUTANE UKU SUNA SAMUN TAIMAKON ALLAH:

1- Mutumin da yake Neman aure Don ya kare mutuncin kansa
2- Mutumin da ya tafi jihadi, Domin daukaka kalmar Allah.
3- Bawa wanda aka dora masa fansar kansa.

ABUBUWA UKU NASA ZUCIYA TA GURBACE:
1- Rashin yarda da kaddara.
2- Aibata bayin Allah na kwarai
3- Wulakanta Iyaye
Rariya.


No comments:

Post a Comment