Wednesday, 29 May 2019

Obasanjo ya tsallake hadarin jirgin sama da kyar


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya tsalllake rijiya da baya a wani hadarin da jirgin sama ya kusa yi a filin sauka da tashin jiragen jihar Legas a yau Laraba.

Jirgin na dauke da fasinjoji 393 kuma ya taso ne daga birnin Addis-Ababa na kasar Ehiopia zuwa Najeriya, Kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

Da yake bayar da labarin yanda lamarin ya faru wani wakilin kamfanin NAN din wanda shima yana cikin jirgin yace direban jirgin ya sauka a filin jirgin saman Legas ne ba daidai ba, da ya lura da hakan zai iya kawo tangarda shine ya sake tashi sama da jirgin inda yayi ta shawagi dashi a sama kamin daga baya ya samu sauke shi cikin nasara.

No comments:

Post a Comment