Friday, 10 May 2019

Ostiriya ta hana yara kanana daura dankwali a makarantun firamare

Gwamnati mai tsaurin ra'ayi ta Ostiriya ta samar da dokar hana yara mata daura dankwali a makarantun firamaren kasar inda majalisar dokoki ta amince da dokar.


Sakamakon yadda jam'iyyun SPO da NEOS suka nuna rashin amincewa da dokar a majalisa ya sanya ta zama doka 'yar karama.

Dokar ta bayyana cewar "Har zuwa yara kanana mata su kai shekaru 10 da haihuwa ba za su dinga daura dankwali ba ko saka wani tufafi da zai bayyana Addinin da suke bi ba." 

Gwamnatin mai tsaurin ra'ayi na kare kanta da cewar wannan doka na da manufar taimakawa yaran wajen su shiga cikin al'uma sosai, amma kuma ba a hana amfani da alama mishan da tambarin Yahudu da Kiristoci da Yahudawa suke amfani da su wanda hakan ya sanya ake zargin dokar na nufar Musulmai ne kadai.

Idan dokar ta fara aiki za a ci tarar Yuro 440 ga iyayen da suka ki aiki da ita a kan yaransu mata.

Shugaban Kungiyar Musulman Ostiriya Umit Vural ya mayar da martani ga wannan doka da gwamnati yta samar ta nuna wariya ga Musulmai, kuma a cikin watan Ramadhan.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment