Thursday, 16 May 2019

Real Madrid ce kungiyar da tafi kowace kungiyar kwallon kafa daraja a Duniya

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta koma matsayinta na kungiyar kwallo da ta fi dara a Duniya inda ta kwace matsayin daga hannun Manchester United wadda kamin wannan lokaci itace ke rike da wancan matsayi.Wannan rahoton na zuwane daga Brand Finance, shahararrun masu tantance darajar abubuwa a Duniya wanda duk shekara suke fitar da kungiyoyin kwallo 50 da suka fi dara ja ta hanyar la'akari da kudin shiga da kuma nasarorin da kungiyoyin suka samu.

Ga kungiyoyi 10 da suka fi daraja a Duniya:

10. Tottenham Hotspur: $758m
9. Arsenal: $885m
8. Paris Saint-Germain: $914m
7. Chelsea: $968m
6. Liverpool: $1.19bn
5. Manchester City: $1.26bn
4. Bayern Munich: $1.31bn
3. Barcelona: $1.39bn
2. Manchester United: $1.47bn
1. Real Madrid: $1.65bn

No comments:

Post a Comment