Monday, 6 May 2019

Real Madrid ta doke Villareal tana nan ta uku a La Liga

Real Madrid ta yi nasarar doke Villareal 3-2 a wasan mako na 36 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.


Real ta ci kwallayen ne ta hannun Jesus Vallejo da kuma Mariano Diaz da ya ci guda biyu, yayin da Villareal ta zare biyu ta hannun Gerard Moreno da kuma Jaume Costa.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka buga a gasar ta La Liga bana ranar 3 ga watan Janairu tashi suka yi 2-2.

Saura wasa biyu a kammala La Ligar shekarar nan, wadda Barcelona ta lashe kofin, kuma na 26 jumulla, inda Lionel Messi ya ci na 10 a Camp Nou.

Real tana nan a matakinta na uku da maki 68, ita kuwa Villareal ita ce ta 14 da maki 40.

Sauran wasannin da suka rage wa Madrid sun hada da zuwa gidan Sociedad ranar 12 ga watan Mayu da wasan karshe a Bernabeu da Real Betis ranar 19 ga watan nan.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment