Thursday, 16 May 2019

Real Madrid zata sayar da 'yan wasanta fiye da 10


media
Rahotanni daga Spain sun ce akwai yiwuwar Real Madrid za ta saida ‘yan wasanta da dama bayan kammala karkare kakar wasa ta bana.

Matakin ya zo ne a dai dai lokacin da kocin kungiyar Zinaden Zidane ke shirin aiwatar da yin gagarumin garambawul ga kungiyar, domin maido da karsashin da ta rasa a baya.
‘Yan wasan da ake sa ran Real Madrid za ta saida sun hada da Gareth Bale, James Rodriguez wanda ke zaman aro a Bayern Munich, Jesus Vallejo, Mateo Kovacic, Dani Ceballos, Marcos llorente da kuma Lucas Vazquez.
Sauran yan wasan kuma sun kunshi mai tsaron ragar kungiyar ta Real Madrid Keylor Navas, Brahim Diaz Mariano Diaz sai kuma Oscar Rodriguez.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment