Wednesday, 15 May 2019

Ronaldo na son Juventus ta siyo 'yan wasan Barcelona 3


Rahotanni daga kungiyar kwallon kafa ta Juventus na cewa tauraron kungiyar, Cristiano Ronaldo ya bukaci da ta siyo taurarin 'yan kwallon Barcelona guda 3 idan aka bude kasuwar cinikin 'yan wasa nan gaba kadan.

'Yan wasan da Ronaldo ke so juventus ta siyo daga Barcelona sune, Jasper Cillessen, Ivan Rakitic da Samuel Umtiti, kamar yanda Fox Sports ta ruwaito.

Dama shi Jasper Cillessen tuni ya bayyana aniyarshi ta barin Barca, lura da cewa ba'a cika yi dashi ba.

Lokaci dai be bar komai ba

No comments:

Post a Comment