Friday, 24 May 2019

SABON SALON KARBAR KUDIN FANSA: 'Yan Kasuwa Ku Ake Fako Sai Ku Kula

Masu garkuwa da mutane sun canza tsohon salon da aka san su da shi, na karbar kudin fansa daga hannun iyaye ko 'yan uwan wadanda suka kama.


A yanzu suna amfani da account number (lambar akawun). Sukan turo da ita ne bayan an tsayar da abinda za a ba su domin fansar wanda suka kama.

A hakikanin gaskiya ba a account lambarsu ba ne ta 'yan kasuwa ce. Suna yaudarar 'yan kasuwa ne ta hanyar kulla ciniki da su, bayan ciniki ya fada, su bukaci a basu lambar akawun da zummar za su turawa mai gidansu wanda shi ne zai turo kudin.

Amma a badini abin ba haka yake ba, wanda aka turawa lambar ba mai gidansu bane basu da alaka dashi ta kusa ko ta nesa,bakowa bane face Wanda suka bukaci kudi a wurinsa domin fansar dansa ko Dan uwansa.

Bayan mai fansar dansa ya turo da kudi, dan kasuwa yaji alart, sai su warware cinikin su ce Mai gidansu ya ce ba irin ta ba, ko shi kenan an fasa.

Amma ka yi hakuri za mu zo mu saya dauki dubu dari cikin kudin mun baka kyauta, shi kuma dan kasuwa cikin rawar jiki da murnar ya samu kudi a banza zai dauki ragowar kudinsu ya basu harda godiya.

'Yan kasuwa sai ayi taka tsan-tsan a kiyaye idan haka ta faru daku ayi gaugawar sanar da hukuma domin samar da tsaro da zaman lafiya.

Allah ka zaunar da kasarmu lafiya alfarmar farin Jakada Muhammad (SAW)No comments:

Post a Comment