Monday, 13 May 2019

Sarkin Kano za mu bi ba na gaya ba>>Inji 'Yan Wudik

Biyo bayan kirkirar sabbin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta yi guda hudu, kungiyoyi da dama na al'ummar karamar hukumar Wudil sun bayyana cewa su masarautar Kano za su bi ba ta Gaya ba.  


Da yake jawabi ga manema labarai  'yan lokuta kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na kungiyoyi daban-daban na karamar hukumar Wudil, karkashin shugabancin Malam Yawale Muhammad Idris, sakataren gamayyar masu ruwa da tsakin Wudil, Dokta Baba Sani Wudil, ya ce an kirkiri sabbin masarautun a jihar Kano ba tare da amincewar al'ummar Wudil ba, wanda hakan ya saba wa al'ada da tsohon tarihin mutanen yankin. 

Ya ce tun da fari ma ba su roki hakan ba, kuma da gwamnati ta yanke shawarar hakan ba ta nemi shawararsu ba. Ya kara da fadin cewa sun tabbatar da cewa idan aka bar wannan sabuwar dokar ta tabbata to za ta shafe tsohon tarihin garin. Saboda haka mutanen Wudil ba za su lamunta ba.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment