Friday, 31 May 2019

Sergio Ramos ya ce a Bernabeu yake son kare rayuwarsa ta tamaula

Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos ya ce yana son ya kare rayuwarsa ta kwallon kafa a Real Madrid duk da ana nemansa China.


A ranar Laraba ne Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya ce Ramos ya nemi ya tafi China domin ci gaba da taka leda a Lig din kasar.

"Gaskiya ne an tuntube ni a China, ba zan yi karya ba," a cewar Ramos mai shekara 33, wanda tun 2005 yake murza leda a Real Madrid.


A 2021 kwangilarsa za ta kawo karshe a Real Madrid.

"Buri na a rayuwa shi ne na yi ritaya a Real Madrid"

Perez ya ce Ramos da wakilinsa sun shaida ma sa cewa sun samu kwangila mai karfi daga wata kungiya da ba a bayyana ba a China.

"Na shaida wa Ramos cewa ba zai yiyu Real Madrid ta bar kaftin din ta ya tafi haka nan kawai ba," in ji Perez.

Ramos ya ce bai taba tunanin barin Real Madrid ba ya koma China.

Sannan ya ce ba zai taba komawa kulub din da zai yi hamayya da Real Madrid ba.

Ramos ya taimakawa Real Madrid lashe kofi 20 a shekaru 14 da ya shafe a Bernabeu, da suka kunshi kofin zakarun Turai hudu da La liga hudu.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment