Tuesday, 14 May 2019

Shekarata 13 A Hukumar EFCC Amma Ba Ni Da Motar Hawa Ta Kaina>>CP Wakili

A wata hira da na yi da kwamishinan 'yan sanda na jihar kano CP Muhammad Wakili (SINGAM MAI GASKIYA) ya shaida min cewa ya kwashe shekara 13 a Hukumar Yaki Da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Taannati ta EFCC yana aiki a hukumar, amma bayan ya kammala aiki sakamakon nada shi kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina ba shi da motar hawa tasa ta kansa. 


"Motar ofis nake hawa, kuma Allah bai ba ni ikon mallakar mota ba, haka na hannatawa ofishin EFCC motar su, na bugawa wani kanina ya bani aron motar da za ta kai ni Katsina, bayan ya aiko da motar, sai yaran da suke aiki a karkashina a hukumar ta mu, suka hada kudi suka saya min mota, haka wasu abokaina su ma suka aiko min da mota, shi ya sa nake saka sunana a jikin takardun motata domin na mallake su ne ta halastacciyar hanya "Inji Shi".

CP Wakili yace 26 ga wannan wata ta Mayu zai yi ritaya a aikin dan sanda, inda zai koma garin sa na Gombe ya zauna da mahaifinsa da mahaifiyar sa ya ci gaba da kwasan albarka tunda duk suna raye, sai dai girma ya riskesu. 

Wakili yana da mata daya da yara, sannnan da gida guda daya tal mallakar sa, kusa da Gidan su na gado anan unguwar tudun wada a birnin Gombe. 

Allah ya karawa rayuwa albarka, ya taimaki mai gaskiya, ya hadamu a jannatul fir-dausi gaba dayan mu. Amin.
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Rariya.


No comments:

Post a Comment