Tuesday, 14 May 2019

Shin da gaske Yusuf Buhari ya mallaki biliyoyin daloli?

An rika yada wani labari da ake dangantawa da mujallar Forbes inda aka ruwaito Yusuf Buhari, wato dan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayi na hadu a jadawalin 'ya'yan shugabannin kasashen duniya da suka fi kudi a fadin duniya.


Rahoton ya yi ikirarin cewa Yusuf Buhari ya "mallaki dala biliyan 2.3."

Mutane musamman a kafafen sada zumunta sun rika yada wannan labari a shafukan Facebook da Twitter kuma labari ya samo asali ne daga wasu kafafen yada labarai a Najeriya.


Mene ne gaskiyar wannan ikirarin?
Binciken da kafar yada labarai ta AFP ta yi ya gano cewa labarin bogi ne saboda mujallar Forbes ba ta wallafa wani rahoto da ke cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3.

Mu ma bincikenmu ya nuna cewa babu kanshin gaskiya a wannan labarin don babu wata babbar kafa mai sahihanci da ta wallafa wannan labarin.

Mujallar Forbes ta wallafa jerin sunayen manyan attajiran Afirka na 2019 kuma 'yan Najeriya hudu ne kawai suka shiga jerin. Amma babu Yusuf Buhari a cikinsu.

Wato Alhaji Aliko Dangote wanda ya mallaki dala biliyan 10.3, sai Mike Adenuga wanda ya ke matsayi na biyu kuma ya mallaki dala biliyan 9.2.

Abdulsamad Rabiu (mai kamfanin siminti na BUA) yana matsayi na uku inda ya mallaki dala biliyan 1.6.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment