Tuesday, 7 May 2019

Shugaba Buhari ya gana da shugabar majalisar dinkin Duniya inda ya gaya mata halin da rikicin Boko Haram ya jefa yankin Arewa maso gabas

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da shugabar majalisar dinkin Duniya, Maria Farnanda a ziyarar da ta kawo Najeriya. 
A yayin ganawar tasu shugaban ya bayyana mata cewa, yanayin da sansanin 'yan gudun hijira yake ciki a Najeriya abin tada hankali ne dan akwai akalla kananan yara miliyan 1 da kodai basu san iyayensu ba wasu kuma ba ma susan daga inda suka fito ba.

Ya kara da cewa, rikicin Boko ya latata kayan bukatun rayuwar yau da kullun musamman a yankin Arewa maso gabas inda an ruguza gadoji da makarantu da masallatai da coci-coci da asibitoci dadai sauran gine-gine, ya kara da cewa dan haka Najeriya na maraba da kowane irin taimako daga kungiyoyin kasashen waje.


No comments:

Post a Comment