Monday, 13 May 2019

Shugaba Buhari ya shiryawa manyan jami'an gwamnati shan ruwa a fadarshi

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya shiryawa mataimakinshi, Farfesa Yemi Osinbajo, Shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emifiele da sauransu shan ruwa a fadarshi yau,Litinin.Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya bayanna cewa taron shan ruwan da shugaban kasar ya shirya ya samu halartar manyan ma'aikatan gwamnati, shuwagabannin hukumomin tsaro da sauran wasu manyan ma'aikatan gwamnatin tarayya.


No comments:

Post a Comment