Wednesday, 29 May 2019

Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa na farko da bai gabatar da jawabin karbar mulki ba: Ya zo da motar miliyan 61 wajan rantsarwar: An kunyatar da Shugaban APC: Yakubu Gowon ne tsohon shugaban kasa daya tilo da ya halarci bikin

A bikin rantsar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da aka yi yau a zango na biyu na mulkinshi, cikin tsaffin shuwagabannin da ake dasu a Najeriya, Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ne kadai ya samu halartar bikin.Olusegun Obasanjo, Abdulsalam Abubakar, Goodluck Jonathan da Janar Ibrahim Badamasi Babangida duk basu samu halartar bikinba, saidai dama tun kamin wannan rana fadar shugaban kasa ta bayyana cewa bikin ba za'ayi shagali da yawa ba sai ranar Yuni 12.

Wani abu na biyu da ya dauki hankulan mutane a rantsar da shugaban kasar na yau shine rashin gabatar da jawabin da aka saba bisa al'ada duk shugaban kasar da aka rantsar yana gabatarwa da shugaba Buhari bai yi ba a yau. Hakan yasa ya zama shugaban kasa na farko da aka zaba a karkashin tsarin dimokradiyya da bai gabatar da jawabin karbar mulki ba a ranar da aka rantsar dashi ba.

Hakan ya jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta inda wasu suka bayyana bikin rantsarwar na shugaban na yau a matsayin wani abu na banbarakwai.

Hakanan wani abu daya kara daukar hankula shine yanda aka cire shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole daga kan layin mutanen da zasu tarbi shugaban kasa a filin rantsarwar inda da farko aka ganshi tsaye tare da manyan jami'an tsaro amma daga baya wani jami'in tsaro ya zo ya fitar dashi daga layi, wasu sun bayyana haka da abin kunya ga shi Oshiomholen.

Abu na gaba da ya dauki hankula a wajan rantsar da shugaban da aka yi yau shine, mota ta musamman da shugaban kasar ya zo da ita wajan rantsar dashi, motar dai kirar Maarsandi S Class S 560 ta shekarar 2019 ana sayar da itane akan dala dubu 170,000 wanda idan aka canja kudin zuwa Naira zasu tasamma kwatankwacin miliyan 61,200,000.

An ruwaito cewa motar an yi tane ta musamman dan hawan shugaban kasar.


No comments:

Post a Comment