Wednesday, 15 May 2019

Shugaba Buhari zai tafi Umarah Saudiyya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umarah a ranar Alhamis.


A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar a shafinta na Twitter ranar Laraba, Sarki Salman Bin Abdulaziz ne ya gayyaci Buhari don gudanar da aikin.

Sanarwar ta ce: "Shugaba Buhari ya amsa gayyatar da Sarki Salman Bin Abdulaziz ya yi masa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umarah.


"Buhari zai bar Najeriya ranar Alhamis 16 ga watan Mayu, tare da masu taimaka masa na musamman.

"Ana sa ran zai koma gida Najeriya ranar Talata 21 ga watan Mayu."

Shugaba Buhari ya ziyarci kasar ta Saudiyya a watan Fabrairun 2016, inda ya gana da mahukuntar da kuma 'yan kasuwar kasar Qatar game da harkokin tattalin arziki.

Sannan kuma ya gudanar da aikin Umarar tare da gwamnonin Osun da Ogun da Zamfara da Borno da Katsina, da kuma Sarki Muhammadu Sanusi II da Oba na Legas.

Sai dai ziyarar ta wannan karon na zuwa ne mako biyu bayan mahukunta kasar sun sako Zainab Aliyu wata daliba 'yar Najeriya da suka zarga da safarar miyagun kwayoyi bayan shafe wata hudu a tsare.

Musulmi da dama kan yi Umarar cikin watan Ramadan saboda falalar da watan ke da ita.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment