Saturday, 18 May 2019

SIMON LALONG YA ZAMA SHUGABAN KUNGIYAR GWAMNONIN AREWA

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya zama shugaban kungiyar gwamnoni 19 na Arewacin Nijeriya. 


Gwamnan ya zamo shugaban kungiyar gwamnonin bayan da wa'adin shugabancin shugaban kungiyar, Kashim Shettima na jihar Borno, ya kare. 

Da yake karanta sanarwa bayan kammala taron tattaunawar kungiyar gwamnonin, Kashim Shettima ya ce gwamnan zai maye kujerarsa a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment